28 Nuwamba 2015 - 15:10
Iran; ta gargadi kungiyar Da’ish

An dauki matakan tsaro a iyakokin kasar Iran da sauran kasashe domin mai da martini ga duk wani hari na bazata daga ‘yan ta’adda na kungiyar Da’ish.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-mataimakin kwamandan rundunar juyin musulunci a safiyar yau lokacin da yake zagayen aiki akan iyakar kasar ta Iran ya nuna gamsuwarsa a kan matakan tsaro da aka dauka domin ganin an gudanar da taron Arba’in lafiya inda ya kara da cewa; hadin kwiwa tsakani ‘yan sanda da sojoji da kuma dakarun juyin musulunci na samun nasara wajan kiyaye iyakokin kasar daga barazanar makiya.

Janaral Hussain salami ya kuma furta cewa; duk wani yunkuri da ‘yan ta’adda na Da’ish ke shiryawa su tabbata zasu hadu da kwakwaran martini daga jumhuriyar musulunci ta Iran.288